Far 49:6-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Ba zan shiga shawararsu ta asiri ba,Ba kuwa zan sa hannu cikin taronsuba,Gama cikin fushinsu suka kashemutane,Cikin gangancinsu kuma sukagurgunta bijimai.

7. La'ananne ne fushinsu domin maitsanani ne,Da hasalarsu kuma, gama bala'i ce.Zan warwatsa su cikin dukan ƙasarYakubu,In ɗaiɗaitar su su cikin Isra'ilawa.

8. “Yahuza, 'yan'uwanka za su yabeka,Za ka shaƙe wuyan maƙiyanka,'Yan'uwanka za su rusuna agabanka.

9. Yahuza ɗan zaki ne,Ya kashe ganima sa'an nan ya komowurin ɓuyarsa.Yahuza kamar zaki yake,Yakan kwanta a miƙe,Ba mai ƙarfin halin da zai tsokaneshi.

10. Yana riƙe da sandan mulkinsa,Ya sa shi a tsakanin ƙafafunsa,Har Shilo ya zo.Zai mallaki dukan jama'o'i.

11. Zai ɗaure aholakinsa a kurangarinabi,A kuranga mafi kyau,Zai wanke tufafinsa da ruwan inabi,Ruwan inabi ja wur kamar jini.

12. Idanunsa za su yi ja wur saboda shanruwan inabi,Haƙoransa kuma su yi fari fatsaboda shan madara.

Far 49