5. Fir'auna ya ce wa Yusufu, “Mahaifinka da 'yan'uwanka sun zo wurinka.
6. Ƙasar Masar tana gabanka. Ka zaunar da mahaifinka da 'yan'uwanka a ƙasa mai kyau, bari su zauna a ƙasar Goshen. In kuma ka san da waɗansu waɗanda suka dace a cikinsu, ka sa su su lura da shanuna.”
7. Yusufu kuwa ya shigo da Yakubu mahaifinsa, ya tsai da shi a gaban Fir'auna, Yakubu kuwa ya sa wa Fir'auna albarka.
8. Fir'auna kuma ya ce wa Yakubu, “Nawa ne shekarun haihuwarka?”
9. Yakubu ya ce wa Fir'auna, “Shekaruna na zaman baƙuncina, shekara ce ɗari da talatin, shekaruna kima ne cike kuma da wahala, ba su kuwa kai yawan shekarun kakannina ba, cikin baƙuncinsu.”
10. Yakubu kuwa ya sa wa Fir'auna albarka, sa'an nan ya fita daga gaban Fir'auna.
11. Sai Yusufu ya zaunar da mahaifinsa da 'yan'uwansa, ya kuwa ba su mahalli a ƙasar Masar, cikin ƙasa mafi kyau a ƙasar Remesse, kamar yadda Fir'auna ya umarta.
12. Yusufu ya bai wa mahaifinsa da 'yan'uwansa da dukan iyalin gidan mahaifinsa abinci, bisa ga yawan 'ya'yansu.
13. A yanzu cikin ƙasar duka, ba abinci, gama yunwar ta tsananta ƙwarai, har ƙasar Masar da ƙasar Kan'ana suka matsu saboda yunwar.
14. Yusufu kuwa ya ƙwalƙwale dukan kuɗin da yake akwai a ƙasar Masar da a ƙasar Kan'ana, domin hatsin da suka saya. Yusufu kuma ya kawo kuɗin cikin gidan Fir'auna.
15. Sa'ad da aka kashe kuɗin da yake a Masar duka da na ƙasar Kan'ana, Masarawa duka suka zo wurin Yusufu, suka ce, “Ka ba mu abinci, don me za mu mutu a kan idonka? Gama kuɗinmu sun ƙare.”
16. Yusufu ya amsa, ya ce, “Ku ba da shanunku, ni kuwa zan ba ku abinci a madadin shanunku in kuɗinku sun ƙare.”
17. Saboda haka suka kai wa Yusufu dabbobinsu, sai Yusufu ya ba su abinci madadin dawakai da garkunan awaki da na tumaki, da garkunan shanu da na jakai, ya tallafe su da abinci a madadin dabbobinsu duka a wannan shekara.