Far 42:1-3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A sa'ad da Yakubu ya ji akwai hatsi a Masar, sai ya ce wa 'ya'yansa maza, “Me ya sa kuke zuba wa juna ido?

2. Ga shi kuwa, na ji akwai hatsi a Masar, ku gangara ku sayo mana hatsi a can domin mu rayu, kada mu mutu.”

3. Don haka 'yan'uwan Yusufu su goma suka gangara su sayo hatsi a Masar.

Far 42