Far 34:8-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Amma Hamor ya yi magana da su, ya ce, “Zuciyar ɗana Shekem tana begen 'yarku, ina roƙonku, ku ba shi ita aure.

9. Ku yi aurayya da mu. Ku ba mu 'yan matanku, ku kuma ku auri 'yan matanmu.

10. Sai ku zauna tare da mu, ƙasar kuma tana gabanku. Ku zauna a cikinta ku yi sana'a, ku sami dukiya.”

11. Shekem kuma ya ce wa mahaifin Dinatu da 'yan'uwanta, “Bari in sami tagomashi a idanunku, dukan abin da kuka ce kuwa, sai in yi.

12. Ku faɗa mini ko nawa ne dukiyar auren da sadakin, zan kuwa bayar bisa ga yadda kuka faɗa mini, in dai kawai ku ba ni budurwar ta zama matata.”

13. 'Ya'yan Yakubu, maza, suka amsa wa Shekem da mahaifinsa Hamor a ha'ince, domin ya ɓata 'yar'uwarsu Dinatu.

14. Suka ce musu, “Ba za mu iya yin wannan abu ba, mu aurar da 'yar'uwarmu ga marasa kaciya, gama wannan abin kunya ne a gare mu.

15. Ta wannan hali ne kaɗai za mu yarda, wato idan za ku zama kamarmu, ku yi wa dukan mazajenku kaciya.

16. Sa'an nan za mu ba ku auren 'ya'yanmu mata, mu kuma mu auro wa kanmu 'ya'yanku mata. Sai kuwa mu zauna tare da ku, mu zama jama'a ɗaya.

17. Amma idan ba ku saurare mu kun yi kaciya ba, sai mu ɗauki 'yarmu, mu kama hanyarmu.”

Far 34