14. A kwanakin kakar alkama, Ra'ubainu ya fita ya samo manta uwa a saura, ya kawo wa mahaifiyarsa Lai'atu. Sai Rahila ta ce wa Lai'atu, “Ina roƙonki, ɗiba mini daga cikin manta uwar da ɗanki ya samo.”
15. Amma ta ce mata, “Kanƙanen abu ne da kika ƙwace mini mijina? Za ki kuma ƙwace manta uwar da ɗana ya samo kuma?”Rahila ta ce, “To, in haka ne, bari ya kwana tare da ke a daren yau a maimakon manta uwar da ɗanki ya samo.”
16. Sa'ad da Yakubu ya komo daga saura da maraice, Lai'atu ta fita ta tarye shi, ta ce, “Sai ka shigo wurina, gama na riga na ijarar da kai da manta uwar da ɗana ya samo.” Saboda haka ya kwana tare da ita a daren nan.
17. Allah ya saurari Lai'atu, ta kuwa yi ciki ta haifa wa Yakubu ɗa na biyar.
18. Lai'atu ta ce, “Allah ya yi mini sakamako domin na ba da kuyangata ga mijina,” saboda haka ta raɗa masa suna Issaka.
19. Lai'atu ta sāke yin ciki ta kuwa haifa wa Yakubu ɗa na shida.
20. Sai Lai'atu ta ce, “Allah ya wadata ni da kyakkyawar baiwa, yanzu mijina zai darajanta ni, domin na haifa masa 'ya'ya maza shida,” ta raɗa masa suna Zabaluna.
21. Daga baya ta haifi 'ya mace, ta kuwa raɗa mata suna Dinatu.
22. Allah kuwa ya tuna da Rahila, ya saurare ta, ya buɗe mahaifarta.
23. Ta yi ciki ta haifa ɗa, ta ce, “Allah ya kawar da zargina,”
24. ta sa masa suna Yusufu, tana cewa, “Da ma a ce Ubangiji ya ƙara mini wani ɗa!”
25. Bayan da Rahila ta haifi Yusufu, Yakubu ya ce wa Laban, “Ka sallame mu, domin mu tafi gidanmu a ƙasarmu.
26. Ka ba ni matana da 'ya'yana waɗanda na yi maka barantaka saboda su, ka bar mu mu tafi, ka dai san ɗawainiyar da na yi maka.”
27. Amma Laban ya ce masa, “Da za ka yarda mini, sai in ce, na fahimta bisa ga istihara, cewa Ubangiji ya sa mini albarka saboda kai.
28. Ka faɗa mini ladanka in ba ka.”
29. Yakubu ya ce masa, “Kai da kanka ka san barantakar da na yi maka, yadda bisashenka suka yawaita a hannuna.
30. Gama kafin in zo, kana da 'yan kima ne, ga shi, sun ƙaru da yawa, Ubangiji kuwa ya sa maka albarka duk inda na juya. Amma yanzu, sai yaushe zan hidimta wa nawa gidan?”
31. Ya ce, “Me zan ba ka?”Yakubu ya ce, “Ba za ka ba ni kome ba, in da za ka yi mini wannan, sai in sāke kiwon garkenka in lura da shi,
32. bar ni, in ratsa garkenka duka yau, in keɓe dukan masu dabbare-dabbare da tumaki babare-babare, da kowane ɗan rago baƙi, da dabbare-dabbare da babare-babare na awaki, waɗannan ne za su zama ladana.
33. Ta haka amincina zai shaide ni a gabanka a sa'ad da ka zo bincike hakkina. Duk wanda aka iske ba dabbare-dabbare ba ne, kuma ba babare-babare ba ne cikin awaki, ba kuma baƙi ba ne a cikin raguna, in aka samu a wurina, sai a ɗauka, na sata ne.”