Far 27:38-41 Littafi Mai Tsarki (HAU)

38. Sai Isuwa ya ce wa mahaifinsa, “Iyakar albarkar da kake da ita ke nan, baba? Har da ni ma ka sa mini albarka, babana.” Isuwa ya ta da murya ya yi kuka.

39. Sai Ishaku mahaifinsa ya amsa masa ya ce,“Ga shi, ni'imar ƙasar za ta nisancimazauninka,Raɓar samaniya can ƙwanƙoli zata nisance ka.

40. Ta wurin takobinka za ka rayuZa ka yi wa ɗan'uwanka barantaka,Amma sa'ad da ka ɓalle,Za ka kakkarye karkiyarsa dagawuyanka.”

41. Isuwa dai ya ƙi jinin Yakubu saboda albarkar da mahaifinsa ya sa masa. Sai Isuwa ya ce a ransa, “Kwanakin makoki domin mahaifina suna gabatowa, sa'an nan zan kashe Yakubu ɗan'uwana.”

Far 27