Far 21:9-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Amma Saratu ta ga ɗan Hajaratu Bamasariya wanda ta haifa wa Ibrahim yana wasa da ɗanta Ishaku.

10. Sai ta ce wa Ibrahim, “Ka kori wannan baiwa da ɗanta, gama ɗan baiwan nan ba zai zama magaji tare da ɗana Ishaku ba.”

11. Abin ya ɓata wa Ibrahim zuciya ƙwarai sabili da ɗansa.

12. Amma Allah ya ce wa Ibrahim, “Kada zuciyarka ta ɓaci saboda yaron da kuma baiwarka. Kome Saratu ta faɗa maka, ka yi yadda ta ce, gama ta wurin Ishaku za a riƙa kiran zuriyarka.

13. Zan kuma yi al'umma daga ɗan baiwar, domin shi ma zuriyarka ne.”

14. Ibrahim ya tashi da sassafe, ya kuma ɗauki gurasa da salkar ruwa, ya bai wa Hajaratu, ya ɗora kafaɗarta. Sai ya ba ta ɗanta, ya sallame ta. Ta tafi ta yi ta yawo cikin jejin Biyer-sheba.

15. Sa'ad da ruwan salkar ya ƙare, sai ta yar da yaron a ƙarƙashin wani ƙaramin itace.

16. Sai ta tafi, ta zauna ɗaura da shi da 'yar rata, misalin nisan harbin baka, gama ta ce, “Don kada in ga mutuwar yaron.” Da ta zauna can daura da shi, sai yaron ya ta da muryarsa ya yi ta kuka.

17. Allah kuwa ya ji muryar yaron, mala'ikan Allah kuma ya kira Hajaratu daga sama, ya ce mata, “Me yake damunki, Hajaratu? Kada ki ji tsoro gama Allah ya ji muryar yaron a inda yake.

18. Tashi, ki ɗauki yaron, ki rungume shi da hannunki gama zan maishe shi babbar al'umma.”

19. Sai Allah ya buɗe idanunta, ta ga rijiyar ruwa, ta kuwa tafi, ta cika salkar da ruwa ta ba yaron ya sha.

20. Allah kuwa yana tare da yaron, ya kuwa yi girma, ya zauna a jeji, ya zama riƙaƙƙen maharbi.

21. Ya zauna a jejin Faran. Sai mahaifiyarsa ta auro masa mata daga ƙasar Masar.

22. A lokacin nan fa, ya zamana Abimelek, da Fikol shugaban sojojinsa ya zo ya ce wa Ibrahim, “Allah yana tare da kai cikin sha'aninka duka,

23. don haka, yanzu sai ka rantse mini da Allah, cewa ba za ka ci amanata, ko ta 'ya'yana, ko ta zuriyata ba, amma kamar yadda na riƙe ka cikin mutunci, haka za ka yi da ni da ƙasar da ka yi baƙunta a ciki.”

24. Sai Ibrahim ya amsa, “I, zan rantse.”

Far 21