32. Saboda haka suka yi alkawari a Biyer-sheba. Sai Abimelek, tare da Fikol shugaban sojojinsa, ya tashi ya koma ƙasar Filistiyawa.
33. Ibrahim kuma ya dasa itacen tsamiya a Biyer-sheba, a can ya yi kira bisa sunan Ubangiji, Allah Madawwami.
34. Ibrahim kuwa ya daɗe yana baƙunci a ƙasar Filistiyawa.