17. Allah kuwa ya ji muryar yaron, mala'ikan Allah kuma ya kira Hajaratu daga sama, ya ce mata, “Me yake damunki, Hajaratu? Kada ki ji tsoro gama Allah ya ji muryar yaron a inda yake.
18. Tashi, ki ɗauki yaron, ki rungume shi da hannunki gama zan maishe shi babbar al'umma.”
19. Sai Allah ya buɗe idanunta, ta ga rijiyar ruwa, ta kuwa tafi, ta cika salkar da ruwa ta ba yaron ya sha.
20. Allah kuwa yana tare da yaron, ya kuwa yi girma, ya zauna a jeji, ya zama riƙaƙƙen maharbi.
21. Ya zauna a jejin Faran. Sai mahaifiyarsa ta auro masa mata daga ƙasar Masar.