Far 16:5-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Sai Saraya ta ce wa Abram, “Bari cutar da aka cuce ni da ita ta koma kanka! Na ba da baranyata a ƙirjinka, amma da ta ga ta sami ciki, sai tana dubana a raine. Ubangiji ya shara'anta tsakanina da kai.”

6. Amma Abram ya ce wa Saraya, “Ga shi, baranyarki tana cikin ikonki, yi yadda kika ga dama da ita.” Saraya ta ƙanƙanta ta, sai Hajaratu ta gudu daga gare ta.

7. Mala'ikan Ubangiji kuwa ya sami Hajaratu a gefen wata maɓuɓɓugar ruwa a jeji, wato maɓuɓɓugar da take kan hanyar Shur.

8. Sai ya ce, “Ke Hajaratu, baranyar Saraya, ina kika fito, ina kuma za ki?”Ta ce, “Gudu nake yi daga uwargijiyata Saraya.”

9. Mala'ikan Ubangiji ya ce mata, “Koma wurin uwargijiyarki, ki yi mata ladabi.”

Far 16