Far 16:12-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Zai zama mutum ne mai halin jakin jeji, hannunsa zai yi gāba da kowane mutum, hannun kowane mutum kuma zai yi gāba da shi. Zai yi zaman magabtaka tsakaninsa da 'yan'uwansa duka.”

13. Sai ta kira sunan Ubangiji wanda ya yi magana da ita, “Kai Allah ne mai gani,” gama ta ce, “Ni! Har na iya ganin Allah in rayu?”

14. Domin haka aka kira sunan rijiyar, Biyer-lahai-royi, tana nan tsakanin Kadesh da Bered.

Far 16