Far 15:1-4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Bayan waɗannan al'amura, maganar Ubangiji ta zo ga Abram cikin wahayi cewa, “Abram, kada ka ji tsoro, ni ne garkuwarka, kana da lada mai yawa.”

2. Amma Abram ya ce, “Ya Ubangiji Allahna, me za ka ba ni, ga shi kuwa, ba ni da ɗa? Ko kuwa Eliyezer na Dimashƙu ne zai gāje ni?”

3. Abram kuma ya ce, “Ga shi, ba ka ba ni zuriya ba, ga shi ma wani yaron gidana ne zai gāje ni.”

4. Sai ga maganar Ubangiji ta zo gare shi cewa, “Mutumin nan, ba shi zai gāje ka ba, ɗan cikinka shi zai gāje ka.”

Far 15