23. Serug kuwa ya yi shekara metan bayan haihuwar Nahor, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza.
24. Sa'ad da Nahor ya yi shekara ashirin da tara, ya haifi Tera,
25. Nahor kuwa ya yi shekara Ι—ari da goma sha tara bayan haihuwar Tera, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza.
26. Sa'ad da Tera ya yi shekara saba'in, ya haifi Abram, da Nahor, da Haran.