21. Na kuma yi shelar azumi a bakin rafin Ahawa don mu ƙasƙantar da kanmu a gaban Allah, mu roƙe shi ya kiyaye mu, da 'ya'yanmu, da kayanmu a hanya.
22. Gama na ji kunya in roƙi sarki ya ba mu sojojin ƙasa da na doki su kāre mu daga maƙiya a hanya, da yake na riga na faɗa masa cewa, “Allah yana tare da dukan waɗanda suke nemansa, ikonsa da fushinsa mai zafi kuwa yana kan dukan waɗanda suke mantawa da shi.”
23. Don haka muka yi azumi, muka roƙi Allah saboda wannan, shi kuwa ya ji roƙonmu.
24. Sai na keɓe goma sha biyu daga cikin manyan firistoci, wato Sherebiya, da Hashabiya, da waɗansu goma daga cikin danginsu.