Ezra 7:8-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Ezra kuma tare da su, suka iso Urushalima a watan biyar na shekara ta bakwai ta sarautar sarkin.

9. Suka taso daga Babila a rana ta fari ga watan fari, suka iso Urushalima a rana ta fari ga watan biyar, Allah kuwa yana tare da su.

10. Gama Ezra ya ba da kansa ga yin nazarin dokokin Allah, ya kiyaye su, ya kuma koyar wa Isra'ilawa dokoki da farillan Allah.

11. Wannan ita ce takardar doka da sarki Artashate ya ba Ezra, wanda yake firist da magatakarda, ƙwararre cikin sha'anin dokoki da umarnan Ubangiji a cikin Isra'ilawa.

12. Ta ce, “Daga Artashate, sarkin sarakuna, zuwa ga Ezra firist, masanin shari'ar Allah na Sama.

13. “Yanzu na yi doka, cewa kowane mutum daga cikin mutanen Isra'ila, da firistocinsu, da Lawiyawansu da suke cikin mulkina wanda yake so ya koma Urushalima, sai ya tafi tare da kai.

14. Gama sarki ne da 'yan majalisarsa guda bakwai suka aike ka don ka san irin zaman mutanen Yahuza da na Urushalima game da dokokin Allahnka, waɗanda suke a hannunka,

15. domin kuma ka ba da azurfa da zinariya waɗanda sarki da 'yan majalisarsa suka ba Allah na Isra'ila da yardar ransu, wato Allah wanda Haikalinsa yake a Urushalima,

16. da kuma azurfa da zinariya da za ka samu a dukan lardin Babila tare da hadayu na yardar rai daga mutane da firistoci, hadayun da suka yi wa'adi su bayar da yardar ransu domin Haikalin Allahnsu, da yake a Urushalima.

17. “Da wannan kuɗi ne za ka himmatu, ka sayi bijimai, da raguna, da 'yan raguna, da hadayunsu na gari, da na sha. Za ka miƙa su a bisa bagaden Haikalin Allah da yake a Urushalima.

18. Duk abin da kai da 'yan'uwanka kuka ga ya dace ku yi, sai ku yi shi da sauran azurfa da zinariya bisa ga nufin Allahnku.

19. Kwanonin da aka ba ka domin hidima a Haikalin Allah, sai ka ajiye su a gaban Allah a Urushalima.

Ezra 7