6. Wannan ita ce wasiƙar da Tattenai mai mulkin lardin Yammacin Kogi, da Shetar-bozenai, da abokansu ma'aikatan hukuma waɗanda suke Yammacin Kogi, suka aika wa sarki Dariyus.
7. “Zuwa ga sarki Dariyus, salama gare ka.
8. Muna sanar da sarki, cewa mun tafi lardin Yahuza a wurin Haikalin Allah Mai Girma. Ana ginin Haikalin da manyan duwatsu, ana kuma sa katakai a bango. Aikin yana ci gaba sosai a hannunsu.
9. “Mun yi magana da dattawan, muka tambaye su wane ne ya ba su izini su gina wannan Haikali har su gama bangonsa.
10. Mun kuma tambaye su sunayensu don mu rubuta maka sunayen mutanen da suke shugabanninsu.
11. To, sai suka ce mana, ‘Mu bayin Allah ne wanda yake da sama da ƙasa, muna sāke gina Haikalin da wani babban sarki na Isra'ila ya gina tun shekaru da yawa da suka wuce.
12. Amma saboda kakanninmu suka tsokani Allah na Sama, sai ya bashe su a hannun Nebukadnezzar, Sarkin Babila, mutumin Kaldiya. Shi ne ya lalatar da Haikalin nan, ya kuma kwashe jama'a zuwa Babila.