Ezra 5:15-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Ya ce masa, ya ɗauki waɗannan kwanoni, ya tafi, ya sa su cikin Haikalin da yake a Urushalima, a sāke gina Haikalin Allah a wurin da yake a dā.’

16. Sheshbazzar kuwa ya zo ya aza harsashin ginin Haikalin Allah wanda yake a Urushalima. Tun daga wannan lokaci, har yanzu ana ta gininsa, har yanzu kuma ba a gama ba.

17. Domin haka in ya gamshi sarki, sai a bincike ɗakin littattafan da yake Babila don a gani ko sarki Sairus ya ba da izini a sāke gina wannan Haikalin Allah a Urushalima. Bari sarki ya aiko mana da abin da ya gani a kan wannan al'amari.”

Ezra 5