Ezra 4:9-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Sa'an nan Rehum shugaban sojoji ya rubuta tare da Shimshai magatakarda,da abokansu, da alƙalai, da masu mulkin larduna, da ma'aikatan hukumomi, wato mutanen Farisa, da na Erek, da na Babila, da na Shusha a ƙasar Elam,

10. da sauran al'ummai, waɗanda mai girma, Asnaffar, ya kwaso, ya zaunar da su a biranen Samariya, da sauran wurare na Yammacin Kogi.

11. Ga abin da suka rubuta.“Gaisuwa daga talakawanka, mutane na hayin Kogin zuwa ga sarki Artashate.

12. “Muna sanar da sarki, cewa Yahudawan nan waɗanda suka fito daga gare ka suka zo wurinmu, sun tafi Urushalima, suna sāke gina mugun birnin nan na tawaye, sun fara gina garun, ba da jimawa ba za su gama ginin.

13. Sarki ya sani fa, idan an sāke gina birnin, aka kuma gama garun, ba za su biya haraji ko kuɗin shiga da fita na kaya ko kuɗin fito ba, baitulmalin sarki za ta rasa kuɗi ke nan.

14. Da yake muke cin moriyar fāda, ba daidai ba ne mu bari a raina sarki. Saboda haka muke sanar da sarki,

Ezra 4