21. Saboda haka sai ka umarci waɗannan mutane su daina gina birnin nan, sai lokacin da na ba da umarni.
22. Ka kula fa, kada ka yi kasala a wannan al'amari, don me ɓarna za ta bunƙasa har ta cuci sarki?”
23. Sa'ad da aka karanta wa Rehum, da Shamshai magatakarda, da abokansu, wasiƙar sarki Artashate, suka hanzarta suka tafi wurin Yahudawa a Urushalima, suka gwada musu iko, suka tilasta musu su daina ginin.
24. An tsai da aikin Haikalin Allah a Urushalima, sai a shekara ta biyu ta sarautar Dariyus Sarkin Farisa.