1. Da tsayawar watan bakwai, sai mutanen Isra'ila waɗanda suka riga suka koma garuruwansu, suka taru gaba ɗaya a Urushalima.
2. Sai Yeshuwa ɗan Yehozadak tare da 'yan'uwansa, firistoci, da Zarubabel ɗan Sheyaltiyel tare da 'yan'uwansu, suka tashi suka gina bagaden Allah na Isra'ila domin a miƙa hadayu na ƙonawa kamar yadda aka rubuta a dokokin Musa, mutumin Allah.
3. Suka ta da bagaden a wurinsa domin suna jin tsoron mutanen ƙasar. Suka miƙa wa Ubangiji hadayu na ƙonawa safe da yamma.