9. Yawan kayayyakin ke nan, kwanonin zinariya guda talatin, da kwanonin azurfa guda dubu (1,000), da wuƙaƙe guda ashirin da tara,
10. da finjalai na zinariya guda talatin, da tasoshi na azurfa ɗari huɗu da goma, da waɗansu kayayyaki guda dubu (1,000).
11. Jimillar kayayyakin duka, na zinariya da na azurfa, dubu biyar da arbaminya (5,400). Sheshbazzar ya tafi da waɗannan kayayyaki duka tare da kamammun da suka komo daga Babila.