Ezra 1:6-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Dukan waɗanda suke kewaye da su, suka taimake su da azurfa, da zinariya, da kayayyaki, da dabbobi, da abubuwa masu daraja, da kyautai na yardar rai.

7. Sarki Sairus kuma ya fito da kayayyakin Haikalin Ubangiji, waɗanda Nebukadnezzar ya kwashe daga Urushalima ya ajiye su a haikalin gumakansa.

8. Sairus Sarkin Farisa ya sa ma'aji, Mitredat, ya fito da kayayyakin, ya ƙidaya wa Sheshbazzar, shugaban Yahuza.

Ezra 1