Ez 40:37-44 Littafi Mai Tsarki (HAU)

37. Ginshiƙai suna fuskantar filin da yake waje. Aka zana siffar itatuwan dabino a kan ginshiƙanta a kowane gefe. Ita ma matakanta takwas ne.

38. Akwai ɗaki, wanda ƙofarsa take duban ginshiƙan gyaffan ƙofofin, a wurin ake wanke hadayar ƙonawa.

39. A shirayin ƙofar akwai tebur biyu a kowane gefe, inda ake yanka hadayar ƙonawa, da hadaya don zunubi da laifi.

40. Akwai tebur biyu a sashin waje na shirayin ƙofar arewa, akwai kuma waɗansu tebur biyu a ɗayan sashin shirayin ƙofar.

41. A gab da ƙofar akwai tebur huɗu, a waje ɗaya kuma akwai huɗu. Duka guda takwas ke nan, inda za a riƙa yanka dabbobin da za a yi hadaya da su.

42. Akwai kuma tebur huɗu da aka yi da sassaƙaƙƙun duwatsu, tsawon da faɗin kowanne kamu ɗaya da rabi rabi ne, tsayi kuwa kamu guda ne. A nan za a ajiye kayan yanka hadayar ƙonawa, da ta sadaka.

43. Aka kakkafa ƙugiyoyi kewaye da cikin ɗakin, tsawonsu taƙi-taƙi. Za a riƙa ajiye naman hadaya a kan teburorin.

44. Ya kai ni fili na can ciki, sai ga ɗakuna biyu a filin. Ɗaya yana wajen ƙofar arewa, yana fuskantar kudu. Ɗayan kuma yana wajen ƙofar kudu yana fuskantar arewa.

Ez 40