1. A ranar goma ga wata na farko a shekara ta ashirin da biyar ta zamanmu a bautar talala, a shekara ta goma sha huɗu da cin birnin, ikon Ubangiji ya sauko a kaina.
2. A cikin wahayi, sai Allah ya kai ni ƙasar Isra'ila, ya zaunar da ni a kan wani dutse mai tsayi ƙwarai, inda na ga wani fasali kamar birni daura da ni.
3. Sa'ad da ya kai ni can sai ga wani mutum, kamanninsa sai ka ce tagulla, yana riƙe da igiyar rama da wani irin ƙara na awo a hannunsa, yana tsaye a bakin ƙofa.