1. Ubangiji ya kuma yi magana da ni, ya ce,
2. “Ɗan mutum, ka fuskanci Dutsen Seyir, ka yi annabci a kansa.
3. Ka faɗa masa, ni Ubangiji Allah na ce,Ga shi, ina gāba da shi, wato Dutsen Seyir.Zan miƙa hannuna gāba da shi,Zan maishe shi kufai, in lalatar da shi.
4. Zan lalatar da biranensa,In maishe su kufai marar amfani,Sa'an nan zai sani ni ne Ubangiji.
5. “Saboda ya riƙe ƙiyayya din din din, ya ba da mutanen Isra'ila domin a kashe su da takobi a lokacin masifarsu, da lokacin da adadin horonsu ya cika,