1. A kan rana ta goma sha biyu ga watan goma a shekara ta goma, sai Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce,
2. “Ɗan mutum, ka fuskanci Fir'auna Sarkin Masar, ka yi annabci gāba da shi da dukan Masar.
3. Ka yi magana, ka ce, Ubangiji Allah ya ce,‘Ga shi, ina gāba da kai, kai Fir'auna Sarkin Masar,Babban mugun dabba wanda yake kwance a tsakiyar koguna,Wanda yake cewa, Kogin Nilu naka ne, kai ka yi shi.
4. Zan sa ƙugiyoyi a muƙamuƙanka,In kuma sa kifayen kogunanka su manne a ƙamborinka,Zan jawo ka daga cikin tsakiyar kogunanka,Da dukan kifayen kogunanka, waɗanda suka manne a ƙamborinka,