5. Sun yi katakanki da itacen fir na Senir,Sun sari itacen al'ul daga Lebanon don su yi miki jigon jirgin ruwa.
6. Sun yi matuƙan jirgin ruwanki da katakon itacen oak na Bashan.Sun daɓe jirgin ruwanki da itacen kasharina na bakin tekun Kittim,Sa'an nan sun manne masa hauren giwa.
7. An yi filafilan jirgin ruwanki da lilin mai kyau, mai ado daga Masar,Don ya zama alama.An yi tutar jirgin ruwanki da shuɗi da shunayya na gaɓar tekun Elisha.
8. Mazaunan Sidon da Arwad su ne matuƙa,Masu hikima, waɗanda suke cikinki, su ne jagora.
9. Dattawan Gebal da masu hikimarta suna tare da ke,Suna tattoshe mahaɗan katakon jirginki,Dukan matuƙan jiragen ruwa sun zo wurinki don kasuwanci.
10. “ ‘Mutanen Farisa, da na Lud, da na Fut suna cikin sojojinki don su yi miki yaƙi. Sun rataya garkuwoyi, da kwalkwali a cikinki. Sun samo miki daraja.