Ez 25:16-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. domin haka ni Ubangiji Allah zan hukunta Filistiyawa. Zan kashe Keretiyawa, in hallaka sauran mazaunan gāɓar teku.

17. Zan yi musu babbar sakayya da hukunci mai tsanani. Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji, sa'ad da na ɗauki fansa a kansu.”

Ez 25