Ez 21:30-32 Littafi Mai Tsarki (HAU)

30. “‘Ka mai da takobinka cikin kubensa. Zan hukunta ka a ƙasarka inda aka haife ka.

31. Zan zubo maka da fushina, in hura maka wutar fushina. Zan bashe ka a hannun mugaye, gwanayen hallakarwa.

32. Za ka zama itacen wuta, za a zubar da jininka a tsakiyar ƙasar. Ba za a ƙara tunawa da kai ba, ni Ubangiji na faɗa.”’

Ez 21