1. A kan rana ta goma ga watan biyar a shekara ta bakwai, sai waɗansu dattawan Isra'ila suka zo don su yi roƙo a wurin Ubangiji. Suka zauna a gabana.
2. Ubangiji kuwa ya yi magana da ni ya ce,
3. “Ɗan mutum, ka faɗa wa dattawan Isra'ila cewa, ‘Ni Ubangiji Allah na ce kun zo ku yi roƙo a wurina, amma hakika, ba na roƙuwa a gare ku.’
4. “Za ka shara'anta su? Ɗan mutum, shara'anta su. To, sai ka sanar da su abubuwa masu banƙyama waɗanda kakanninsu suka yi.
5. Ka ce musu, ni Ubangiji Allah, na ce a ranar da na zaɓi Isra'ila na ta da hannuna, na rantse wa zuriyar Yakubu, na kuma bayyana kaina a gare su a ƙasar Masar, cewa ni ne Ubangiji Allahnsu,