Ez 16:9-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. “Sa'an nan na yi miki wanka da ruwa, na wanke jinin haihuwarki na shafe ki da mai.

10. Na sa miki rigar da aka yi wa ado, na kuma sa miki takalmin fata, na yi miki ɗamara da lilin mai kyau, na yi miki lulluɓi da siliki.

11. Na kuwa caɓa miki ado, na sa mundaye a hannuwanki, da abin wuya a wuyanki.

Ez 16