1. Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce,
2. “Ɗan mutum, ka sa Urushalima ta san ayyukanta na banƙyama.
3. Ka faɗa wa Urushalima abin da ni Ubangiji Allah na ce mata.”Ubangiji ya ce, “Asalinki da haihuwarki daga ƙasar Kan'ana ne. Mahaifinki Ba'amore ne, mahaifiyarki kuwa Bahittiya ce.
4. Game da haihuwarki kuwa, ran da aka haife ki, ba a yanke cibiyarki ba, ba a kuma yi miki wanka da ruwa don a tsabtace ki ba, ba a kuma goge ki da gishiri ba, ba a naɗe ki cikin tsummoki ba.