19. Kerubobin kuwa suka ɗaga fikafikansu, suka tashi daga ƙasa, suka yi sama a kan idona, suka tafi da ƙafafun gab da su. Suka tsaya a ƙofar gabas ta Haikalin Ubangiji. Ɗaukakar Allah na Isra'ila kuwa tana bisa kansu.
20. Waɗannan su ne talikan da na gani a ƙarƙarshin kursiyin Allah na Isra'ila a bakin kogin Kebar, na kuwa sani su kerubobi ne.
21. Kowannensu yana da fuska huɗu, da fiffike huɗu. A ƙarƙashin fikafikansu suna da hannuwa irin na 'yan adam.
22. Kamannin fuskokinsu kuma daidai yake da kamannin fuskokin da na gani a bakin kogin Kebar. Sai suka tafi, kowa ya nufi gabansa sosai.