14. Kowane kerub yana da fuska huɗu. Fuska ta fari ta kerub ce, fuska ta biyu ta mutum ce, fuska ta uku ta zaki ce, fuska ta huɗu kuwa ta gaggafa ce.
15. Kerubobin kuwa suka tashi sama. Waɗannan su ne talikai huɗu waɗanda na gani a bakin kogin Kebar.
16. Sa'ad da kerubobin suka tafi, ƙafafun kuma sukan tafi tare da su. Sa'ad da suka ɗaga fikafikansu don su tashi daga ƙasa zuwa sama, ƙafafun kuma ba su barinsu.
17. Sa'ad da suka tsaya cik, sai ƙafafun su ma su tsaya cik, sa'ad da suka tashi sama, sai su kuma su tashi tare da su, gama ruhun talikan yana cikinsu.
18. Sai ɗaukakar Ubangiji ta tashi daga bakin ƙofar Haikalin, ta tsaya bisa kerubobin.