Esta 9:2-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Sai Yahudawa suka taru a biranensu a dukan lardunan sarki Ahasurus, don su tasar wa waɗanda suke so su yi musu ɓarna. Ba wanda ya tasar musu gama tsoronsu ya kama mutane.

3. Dukan sarakunan larduna, da hakimai, da masu mulki, da ma'aikatan sarki, suka taimaki Yahudawa, gama tsoron Mordekai ya kama su.

4. Gama Mordekai ya zama babban mutum a gidan sarki, ya kuma yi suna a dukan larduna, gama ya yi ta ƙasaita gaba gaba.

5. Yahudawa kuwa suka kashe dukan maƙiyansu da takobi. Suka hallaka maƙiyansu yadda suke so.

6. A Shushan, masarauta kanta, Yahudawa suka hallaka mutum ɗari biyar.

7. Suka kuma kashe Farshandata, da Dalfon, da Asfata,

8. da Forata, da Adaliya, da Aridata,

9. da Farmashta, da Arisai, da Aridai, da Waizata.

10. Su ne 'ya'ya goma na Haman, ɗan Hammedata, maƙiyin Yahudawa, amma ba su washe dukiyarsu ba.

11. A ranar ce aka faɗa wa sarki yawan mutanen da aka kashe a Shushan, masarauta.

12. Sai sarki ya ce wa sarauniya Esta, “A Shushan, masarauta, Yahudawa sun kashe mutum ɗari biyar da kuma 'ya'yan Haman guda goma. Mene ne suka yi a sauran lardunan sarki? Mece ce kuma bukatarki? Za a yi miki. Mene ne kuma roƙonki? Za a ba ki.”

13. Esta ta ce, “Idan sarki ya yarda, bari a yardar wa Yahudawan da suke Shushan su yi haka gobe, kamar yadda suka yi yau. Bari a rataye gawawwakin 'ya'yan Haman guda goma a bisa gumagumai.”

14. Sarki kuwa ya ce a yi haka ɗin. Sai aka yi doka a Shushan, aka kuwa rataye gawawwakin 'ya'yan Haman guda goma.

15. Yahudawan da suke Shushan kuwa suka taru a rana ta goma sha huɗu ga watan Adar, suka kashe mutum ɗari uku a Shushan, amma ba su washe dukiyarsu ba.

16. Yahudawan da suke cikin lardunan sarki kuma suka taru, suka kare rayukansu, suka ƙwaci kansu daga maƙiyansu. Suka kashe mutum dubu saba'in da dubu biyar (75,000) daga cikin maƙiyansu, amma ba su washe dukiyarsu ba.

Esta 9