10. An yi rubutu da sunan sarki Ahasurus, aka kuma hatimce shi da hatimin zoben sarki. Aka aika da wasiƙun ta hannun 'yan-kada-ta-kwana, waɗanda suka hau dawakai masu zafin gudu da akan mora a aikin sarki.
11. A wasiƙun, sarki ya yardar wa Yahudawan da suke a kowane birni su taru, su kāre rayukansu, su kuma hallaka kowace rundunar mutane da kowane lardi da zai tasar musu, da 'ya'yansu, da matansu, su karkashe su, su rurrushe su, su kuma washe dukiyarsu.
12. Za a yi wannan a dukan lardunan sarki Ahasurus ran goma sha uku ga watan goma sha biyu, wato watan Adar.
13. Sai a ba kowane lardi fassarar dokar, don a yi shelarta ga dukan mutane, Yahudawa kuwa su yi shiri saboda wannan rana, domin su ɗau fansa a kan maƙiyansu.