Esta 5:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A kan rana ta uku sai Esta ta sa rigunan sarautarta, ta tafi, ta tsaya a shirayi na ciki na fādar sarki, kusa da ɗakin sarki. Sarki kuwa yana zaune a gadon sarautarsa, a gidan sarautarsa, daura da ƙofar shiga fāda.

2. Sa'ad da ya ga Esta tana tsaye a shirayin, sai ya miƙa mata sandan zinariya na sarauta, gama ta sami kwarjini a wurinsa. Sai Esta ta matsa kusa ta taɓa kan sandan.

3. Sarki ya ce mata, “Mene ne, sarauniya Esta? Me kike so? Za a ba ki, ko rabin mulkina ma.”

4. Sai Esta ta ce, “Idan sarki ya yarda, bari sarki ya zo tare da Haman yau wurin liyafa da na shirya wa sarki.”

5. Sarki kuwa ya ce, “A zo da Haman maza, mu yi abin da Esta take so.” Sai sarki da Haman suka tafi liyafar da Esta ta shirya.

Esta 5