Da Mordekai ya ji dukan abin da aka yi, sai ya yage tufafinsa, sa'an nan ya sa rigar makoki, ya zuba toka a kā. Ya fita zuwa tsakiyar birni, yana ta rusa kuka da ƙarfi.