1. A shekara ta farko ta sarautar Belshazzar Sarkin Babila, Daniyel ya yi mafarki, ya kuma ga wahayi sa'ad da yake kwance a gadonsa. Sai ya rubuta mafarkin. Ga abin da ya faɗa.
2. Daniyel ya ce, “A wahayi da dare na ga iskar samaniya daga kusurwa huɗu tana gurɓata babbar teku.
3. Sai manyan dabbobi huɗu iri dabam dabam suka fito daga cikin tekun.
4. Kamannin dabba ta fari irin ta zaki ce, amma tana da fikafikan gaggafa. Ina kallo, sai aka fige fikafikanta, aka ɗaga ta sama, aka sa ta tsaya a kan ƙafafu biyu kamar mutum, aka ba ta tunani irin na mutum.
5. “Sai kuma ga dabba ta biyu mai kama da beyar. Gefe guda na jikinta ya ɗara ɗaya. Tana riƙe da haƙarƙari uku a haƙoranta! Sai aka ce mata, ‘Tashi ki cika cikinki da nama.’