Dan 5:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sarki Belshazzar ya yi wa dubban manyan mutanensa liyafa, ya kuwa sha ruwan inabi a gabansu.

2. Da Belshazzar ya kurɓa ruwan inabin, sai ya umarta a kawo tasoshi na zinariya da na azurfa waɗanda Nebukadnezzar ubansa ya kwaso daga Haikali a Urushalima, domin sarki, da manyan mutanensa, da matansa, da ƙwaraƙwaransa su sha ruwan inabi da su.

3. Sai suka kawo tasoshin zinariya da na azurfa waɗanda aka kwaso daga cikin Haikali, wato Haikalin Allah a Urushalima. Sai sarki da manyan mutanensa, da matansa, da ƙwaraƙwaransa, suka yi ta sha da su.

4. Da suka bugu da ruwan inabi, sai suka yi yabon gumakansu na zinariya, da na azurfa, da na tagulla, da na baƙin ƙarfe, da na itace, da na dutse.

5. Nan da nan sai yatsotsin hannun mutum suka bayyana, suka yi rubutu a kan shafen bangon fādar sarkin, wanda yake daura da fitila. Sarki kuwa yana ganin hannun sa'ad da hannun yake rubutu.

6. Sai fuskar sarki ta turɓune, tunaninsa suka razanar da shi, gaɓoɓinsa suka saki, gwiwoyinsa suka soma bugun juna.

Dan 5