10. Mutane da yawa za su tsarkake kansu, su zama masu tsabta tsab tsab, amma mugaye ba za su gane ba, za su yi ta muguntarsu, amma masu hikima za su gane.
11. “Tun daga lokacin da za a hana miƙa hadayar ƙonawa ta yau da kullum, a kafa abin banƙyama, wanda yake lalatarwa, za a yi kwana dubu da ɗari biyu da tasa'in.
12. Masu farin ciki ne waɗanda suka daure, har suka kai ƙarshen kwana dubu da ɗari uku da talatin da biyar.