Dan 11:23-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

23. Daga lokacin da aka ƙulla yarjejeniya da shi, zai yi munafunci. Zai sami iko ta wurin goyon bayan mutane kima.

24. Ba zato ba tsammani zai kai wa lardi mafi arziki hari. Zai aikata abin da kakanninsa ba su taɓa yi ba. Zai rarraba wa mabiyansa kwason yaƙi, da ganima, da dukiya. Zai kuma yi shiri ya kai wa kagara hari amma domin ɗan lokaci ne kawai.

25. “Zai iza kansa ya yi ƙarfin hali ya kai wa sarkin kudu yaƙi da babbar rundunar soja. Sarkin kudu zai haɗa babbar rundunar soja mai ƙarfi don yaƙin, amma ba zai iya karo da shi ba, domin za a shirya masa maƙarƙashiya.

26. Waɗanda suke na jikinsa, su ne za su zama sanadin faɗuwarsa. Za a kashe rundunar sojojinsa, a shafe su duk.

27. Sarakunan nan biyu sun sa mugunta a ransu. Za su zauna a tebur guda su yi ta shara wa juna ƙarya, amma a banza, gama lokacin da aka ƙayyade bai yi ba tukuna.

Dan 11