20. Ko na yi zunubi ina ruwanka,Kai mai ɗaure mutane?Me ya sa ka maishe ni abin bārata?Ni wani babban kaya mai nauyi ne a gare ka?
21. Ba za ka iya gafarta mini zunubina ba?Ba za ka kawar da kai ga muguntar da na aikata ba?Ba da daɗewa ba zan rasu in koma a ƙura,Lokacin da ka neme ni ba za ka same ni ba.”