1. Ubangiji ya yi wa Ayuba magana.
2. “Mai neman sa wa wani laifi ya jā da Mai Iko Dukka?Wanda yake gardama da Allah, bari ya ba da amsa.”
3. Ayuba ya amsa wa Ubangiji ya ce,
4. “Ai, ni ba a bakin kome nake ba,Wace amsa zan ba ka?Na rufe bakina na yi gam.