Ayu 39:9-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. “Kutunkun ɓauna zai yarda ya yi maka aiki?Zai yarda ya kwana ɗaya a dangwalinka?

10. Ka iya ɗaure shi da igiya a kwarin kunya?Ko kuwa zai yi maka kaftu a fadamarka?

11. Za ka dogara gare shi saboda tsananin ƙarfinsa?Za ka kuma bar masa aikinka?

12. Ka gaskata zai komo,Ya kawo maka hatsi a masussukarka?

13. “Jimina takan karkaɗa fikafikanta da alfarma!Amma ba su ne gashin fikafikan ƙauna ba.

14. Jimina takan bar wa ƙasa ƙwayayenta,Ta bar ƙasa ta ɗumama su.

15. Takan manta wani ya iya taka su su fashe,Ya yiwu kuma wani naman jeji ya tattake su.

16. Takan yi wa 'ya'yanta mugunta,Sai ka ce ba nata ba ne,Ko da yake ta sha wahala a banza,Duk da haka ba ta damu ba.

17. Gama Allah bai ba ta hikima ba,Bai kuwa ba ta fahimi ba.

18. Amma sa'ad da ta sheƙa a guje,Takan yi wa doki maguji da mahayinsa dariya.

Ayu 39