7. Idan kai adali ne da me ka ƙara masa,Ko kuwa me ya samu daga gare ka?
8. Muguntarka ta shafi mutum ne kamarka,Haka kuma adalcinka ya shafi ɗan adam ne kawai.
9. “Saboda yawan zalunci, jama'a sukan yi kuka,Suka nemi taimako, saboda matsin masu ƙarfi.
10. Amma ba su juyo wurin Allah Mahaliccinsu ba,Wanda yakan sa a raira waƙa da dare,
11. Wanda yake koya mana fiye da namomin jeji da suke a duniya,Wanda ya sa muka fi tsuntsayen sama hikima.