Ayu 27:12-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Ga shi kuwa, dukanku kun gani da kanku,Me ya sa kuka zama wawaye?

13. “Wannan shi ne rabon mugaye daga wurin Allah,Gādo ne kuma wanda azzalumai za su karɓa daga wurin Mai Iko Dukka.

14. Idan 'ya'yansu sun riɓaɓɓanya za su zama rabon takobi,Zuriyarsu kuwa ba za su sami isasshen abinci ba.

Ayu 27