4. Kana tsammani wane ne zai ji maganganunka duka?Wane ne ya iza ka ka yi irin wannan magana?
5. “Lahira tana rawa,Mazaunanta suna rawar jiki don tsoro.
6. Lahira tsirara take a gaban Allah,Haka kuma Halaka take a gaban Allah.
7. Allah ne ya shimfiɗa arewa a sarari kurum,Ya rataya duniya ba bisa kan kome ba.
8. Allah ne ya cika gizagizai masu duhu da ruwa,Girgijen kuwa bai kece ba.
9. Ya rufe kursiyinsa, ya shimfiɗa girgije a kansa.
10. Ya shata da'ira a kan fuskar teku,A kan iyakar da take tsakanin haske da duhu.
11. Ginshiƙan samaniya sun girgiza,Sun firgita saboda tsautawarsa.