Ayu 25:3-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Akwai wanda zai iya ƙidaya mala'ikun da suke masa hidima?Akwai wurin da hasken Allah bai haskaka ba?

4. Akwai wanda ya isa ya zama adali,Ko mai tsarki a gaban Allah?

5. Hasken wata ba haske ba ne a gare shi,Ko taurari ma ba su da tsarki a gabansa.

6. To, mutum fa? Ai, wannan tsutsa ne, ɗan ƙwaro kawai.Me mutum ya daɗa a gaban Allah?”

Ayu 25