Ayu 20:4-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. “Hakika ka sani tun daga zamanin dā,Sa'ad da aka fara sa mutum a duniya,

5. Ba wani mugun mutum wanda ya taɓa daɗewa da farin ciki.

6. Mai yiwuwa ne ya ƙasaita, ya zama kamar hasumiya a sararin sama.Ya ƙasaita har kansa ya taɓa gizagizai.

7. Amma zai shuɗe kamar ƙura.Waɗanda dā suka san shi,Za su yi mamaki saboda rashin sanin inda ya tafi.

Ayu 20